29 Oktoba 2020 - 13:38
Mutane Biyu Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Sami Raunuka A Wani Hari Da Aka Kai Faransa

Rahotanni daga kasar Faransa sun bayyana cewar akalla mutane biyu sun mutu kana wasu kuma sun sami raunuka biyo bayan wani hari da wuka da aka kai birnin Nice na kasar Faransan a yau Alhamis.

ABNA24 : Yayin da yake sanar da hakan cikin wani sako na Twitter da ya fitar, Magajin garin na Nice, Christian Estrosi ya bayyana cewar harin ya faru ne kusa da cocin Notre Dame church na birnin, sannan kuma tuni ‘yan sanda suka kama mutumin da ya kai harin.

‘Yan sandan birnin dai sun tabbatar da mutuwar mutane biyu da kuma samun raunin wasu yayin wannan harin.

Ministan harkokin cikin gida na ƙasar Faransan ya buƙaci jama'ar ƙasar da su ƙaurace wa wurin da aka kai harin a daidai lokacin da ya sanar da cewa yana gudanar da taro na gaggawa kan lamarin.

Har ya zuwa yanzu dai ba a tantance manufar kai wannan harin ba, ko yana da alaka da zanen batanci da aka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a) a kasar da kuma kalaman da shugaban kasar Emmanuel Macron yayi na nuna goyon baya ga zaben batancin da aka yi wa Ma’aiki (s.a.w.a) a kasar ta Faransa ba.

342/